Takaitaccen Bayani Akan Liquidity
“Banso na kara magana akan liquidity ba, amma Kasancewar har yanzu akwai bayanin da nake son yiwa mutane wanda ba’ayi ba kuma yana da mahimmanci shiyasa zanyi magana”
A taikace dai duk lokacin da za’a yi bayani akan liquidity a gurin yan crypto zaka masa bayani kala biyu ne.
(1) Na farko ma’anar liquidity ta fuskar zamantakewa ta dan adam.
(2) Na biyu ma’anar liquidity ta fuskar kasuwancin cryptocurrency.
Matsalar da ake samu shine, a koyaushe idan yan crypto suka tashi fassara liquidity toh suna masa fassarar crypto ne. Amma abinda mutanen mu yan crypto bamu fahimta ba shine. Yanzu kasuwar cryptocurrency tayi girman da ta wuce ayi mata irin liquidity din da akeyi a baya, yanzu tana buqatar liquidity ta fuskar ma’ana da zamantakewar dan adam.
Bari mu fara bayanin liquidity a ta fuskar zamantakewar dan adam.
Da farko bari mu fara daukar misali guda biyu na liquidity ta fuskar zamantakewa ta dan adam. Misalin da zamu dauka shine Daddawa wacce ake miya sa ita, da kuma kayan rafta (jari bula).
Ina da tabbacin kafin yanzu akwai lokacin da mutane basa saka kudi su siyi daddawa, kawai hada ta akeyi ayi miya. A hankula kayan da ake amfani dasu (ingredients) gurin yin daddawa sai suka fara karanci, kaga a nan an samu (scarcity). Daga nan sai ya zamana mutanen da suke iya samo wadannan ingredients din har su hada daddawa kadan ne. Hakan yasa a gurin su ta zama kadara (Asset).
Daga bangare guda kuma mutane sun saba amfani da daddawa sun fahimci mahimmancin ta, kaga a nan ta samu mahimmanci (value is created), saboda haka sai suka fara cire kudi suna siyanta. Daga nan sai daddawa ta zama tradable assets, saboda tana da value and its scarce kuma mutane na iya holding dinta, shiyasa har iyayen mu mata suke ajiye ta idan tayi tsada su fito su siyar da itasu siyar.
Misali na biyu kuma duk wanda yake rayuwa a ghetto kamar ni din nan yasan rafta (jari bola), kuma yasan lokacin da dadewa a rafta idan kaje karafuna, aluminium da bronze (jar waya) zaka dinga gani. Amma kuma yanzu idan kaje rafta duk wadannan sunyi karanci, yanzu rubba, leda da kwali zaka dinga gani. Zaka tambayi kanka meyasa a baya babu su sai yanzu?🤔
Amsar itace a lokacin nan ledoji, rubba da kwali basu da liquidity. Yanzu ne suk samu liquidity saboda fasahar recycling din su sa kamfanunuwa sukeyi, hakan ya samar musu da value kuma suka zama assets, shiyasa har kake iya tara su kaje ka kai rafta ka karbi kudi. Wannan recycling din da akeyi na rubber da kwali da leda shi yayi creating musu value suka zama asset har a kwana a tashi suka zama tradable asset a kasuwar rafta.
Banbancin kayan rafta na yanzu (leda, roba, kwali) da daddawa shine su suna da yawa a gari, bi ma’ana (Total supply) dinsu yayi yawa shiyasa basu kaita daraja ba, saboda duk da kasancewar suma sun zama tradable assets, amma they are not scarce. Shiyasa ko a raftar idan ka duba zakaga duk abinda total supply dinsa yayi yawa to zakaga bashi da kima sosai.
Misali a rafta jan karfe yafi komai daraja, sai normal karfe, sai aluminum. Daga nan sai kwali, roba sai kuma leda itace ta karshe. Kuma idan ka duba zakaga duk abinda yafi yawa shine bashi da kima. Kaga kenan ashe total supply yana iya jawo kima (value) ko kuma rage kima. Sannan ana amfani da karfe a gurare da yawa fiye da leda, shiyasa ya kara fin leda daja.
Daidai yake da kace anyi creating ma karfe (Uses cases) fiye leda hakan ya jawo ya kara yin wahala (scarcity) samu. Sannan yanzu ka fuskanci ashe Use Case yana karawa abu daraja, sannan rashin sa na iya karya daraja. Maybe da ace nan gaba za’a ci gaba da creating abubuwan amfani (Use cases) da leda masu daraja zata iya zuwa tafi karfe tsada.
Wannan a takaice kenan, idan ka fahimta to zaka gane cewar ashe lallai komai kafin ya zama tradable asset yana buqatar liquidity dinnan.
Insha Allah zamuyi bayanin liquidity bangaren cryptocurrency.
Bissalam
Wallahu ya’alamu……..
Bashir Maawi
.jpeg)